Miliyoyin Daloli Da Shugaba Mugabe Ya Bari Na Tada Kayar Baya

Wata kafar yada labarai a kasar Zimbabwe ta bayyanar da cewar, an samu tsabar kudi da suka kai dalar Amurka miliyan goma $10M cikin asusun bankin tsohon shugaban kasar Robert Mugabi. A cewar kafar bayanin ya fito da cikin wata wasika da ‘yar mamacin ta fitar.

Daloli

Margayin ya bar kudi dalar Amurka $10M, da wasu karin gidaje, kamar yadda rahotanni suka nuna a ranar Talata. Jaridar Herald News mallakar gwammatin kasar Bona Chikore ce ta bayyana haka ga babbar kotun daukaka kara, a yayin da iyalansa su ka kasa gano inda dukiyoyinsa su ke.

Sanarwar ta ce kudaden na cikin wani asusun banki a kasashen waje.

Mugabe wanda ya rasu a kasar Singapore, bayan wata kajeriuwar rashin lafiya, ya bar gidaje hudu a Harare babban birnin kasar Zimbabwe, motoci 10, fili mai girman hekta 27, tare da lambu a kauyensa da aka birne shi.

Daga cikin kadaroronsa, akwai wani katafaren gida da ake yiwa lakabi da Blue Roof a birnin Harare. Wannan duk ba’a ambaci gonannaki da dama da aka taba ruwaitowa ya mallaka ba, ko kuma gidan madarar shanu da su ke tafiyarwa da matarsa Grace Mugabe, ko wasu karin kudarori da ke wajen kasar Zimbabwe.

Bisa dokar kasar Zimbabwe, duk wanda ya rasu ya bar gidaje, ba tare da barin wasiya ba, akan raba gadon ne ga iyalanshi. Cikin wata wasika da ya rubutowa kotu, lauyansa mai suna Terrence Hussein, kamar yadda jaridar ta ruwaito, ya ce her yanzu ba su gano wata wasiya da marigayin ya bari ba, amma sun aika takardu ga wasu cibiyoyin shari’a.