Mota Ta Farko Mara Rufin Sama, Gilashin Gaba Ko Radiyo

Mota kirar McLaren Elva

Wani kamfanin kera motoci na Burtaniya, McLaren Elva ya kera wata mota wadda babu irinta a fadin duniya, kudin motar ya kai dalar Amurka dala miliyan $1.7 kwatankwacin Naira miliyan dari shida.

Motar dai ba ta dauke da radiyo, kana ba’a kera jikinta da karfe ba, an yi amfani da wani nau’in katako ne wajen kerata, kana ba ta da runfa, balle gilashin gaba. Ita dai motar ba kamar sauran motoci da aka saba da su ba ne wajen bude samanta ko kullewa a duk lokacin da aka bukaci hakan.

A duk lokacin da mutun ke tsuga gudu da ya wuce tafiya kimanin kilomita 25 a cikin sa’a daya, wasu na’urorin da ke cikin motar za su fito don su rage ma mutun karfin iska da ke bugun fuskar mutun. Motar na da wani tsari da ke maida iska gefe ba tare da ta damu mutanen da ke cikin motar ba.

Motar na da karfin dawakai 804, karfin inji kuwa ya kai na wuta 8, injin din motar na karkashin kujerun direba da mai zaman banza. Ta na gudun kimanin kilomita 60 cikin sa’a daya, kamfanin ya kera guda 399 kacal na wannan motar, za kuma a fara amfani da nau’in motocin cikin shekara mai zuwa.