Muhammada Ali: 1942 - 2016

An hanifi Muhammada Ali a Louisville dake birnin Kenturkey, kuma mahaifinsa sana’ar penti ya ke, ya kuma tsunduma cikin harkar dambe ne bayan da wasu ‘yan unguwarsu suka sace mai keke.

Muhammad Ali ya canza sunansa daga Cassius Clay zuwa Muhammad Ali a ranar shida ga watan Maris din shekarar 1964 bayan da ya karbi addinin Islama.

Muhammad Ali mutum ne da ake wa kallon mai yawan cika baki da kuma basirar iya sarrafa kalamomi, kamar fitacciyar maganar nan da ya taba yi cewa: “shi yana tashi kamar Malam bude mana littafi , yana kuma harbi kamar zuma.”