Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Kankama

Paul Pgoba na Manchester United.

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Thierry Henry, wanda yanzu yake kasar Belgium bangaren ma'aikantan horas da ‘yan wasa ya amince da ya karbi kungiyar kwallon Kafa ta Aston Vila, a matsayin mai hiraswa inda zai maye gurbin tsohon kocinta Steve Bruce.

Kungiyar Juventus ta ce zata sayar da dan wasanta Miralem Pjanic, mai shekaru 28, da haihuwa domin shirye shiryenta na ganin ta dawo da dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pgoba, wanda ta sayar dashi a shekarun baya.

Dan wasa mai tsaron raga na Liverpool Loris Karius na tunanin barin kungiyar bayan abinda ya kira cin fuska da akai masa na yadda aka sayo mai tsaron raga Alisson daga Roma.

Chelsea, tana shirye shiryen biyan fam miliyan 45 wajan sayen dan wasan baya na Juventus mai suna Daniele Rugani, 23. Bayan haka Chelsea ta sake yin watsi a karo na uku kan tayin da kungiyar Barcelona tayi na fam miliyan 65 domin sayen dan wasanta William.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sayi sabon mai tsaron raga Andriy Lunin daga kungiyar Zorya Luhansk. Dan wasan mai shekara 19 a duniya zai koma Madrid daga kungiyar Zorya Luhansk a kan yarjejeniyar shekara shida. Dan wasan wanda dan kasar Ukraine ne ya taka wa tawagar kasar leda, sau 40 a gasar firimiyar kasar.

A makon jiya ne Madrid, ta sayi matashi dan wasan Brazil Vinicius de Oliveria Júnior daga kulob din Flamengo. Ana yi wa Vinicius mai shekara 18 kallon na daya daga cikin matasan da suka fi haskakawa a fagen wasan kwallon kafa a duniya.

Har yanzu kungiyar Arsenal tana cigaba da zawarcin dan wasan tsakiya na Sevilla Steven Nzonzi, mai shekaru 29, sai dai ta kasa biyan fam miliyan 35 kamar yadda kulob dinsa yake bukatar Chelsea tana bukatar sayen mai tsaron raga na kungiyar AC Milan tsohon dan wasan Liverpool Pepe Reina dan shekaru 35 a duniya akan kudi fam miliyan 9.

Your browser doesn’t support HTML5

Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Kankama