Babban burina shine in koma makaranta domin cigaba da karatu, kuma ina da muradin kasancewar ma’akaciya a asibiti, dalilin haka ya sa bayan dogon lokaci yanzu nake da nufin komawa karatu inji Maryam Mohammad.
Maryam, ta bayyana haka ne a tattaunawar ta da wakiliyar DandalinVOA a Kano, inda ta bayyana cewa bayan ta yi aure har ta haihu, a yanzu kuma ta sami damar komawa karatu, inda ta nemi gurbi a makarantar health technology.
Ta kara da cewa ta dade tana son komawa makaranta amma sai yanzu ne lokacinta yayi, kuma ta zabi wannan fanni ne saboda tana shi’awar taimakawa ‘yan uwanta mata mussaman a asibitoci, wato bangaren lafiya ganin cewa yadda bangaren ke bukatar taimakon mata. Maryam, ta ce babban abin shi’awa shine kowacce mace na bukatar idan ta je asibiti ‘yar uwarta mace ce zata kula da ita.
Daga karshe kuma ta ja hankalin mata mussaman matasa da su jajirce wajen neman ilimi, a kauda wasa sa’annan a duba kwas da zai taimakawa al’uma da kasa tare da duba al’umarka wato yankin da mutum yake da kuma lura da abinda zai amfane su.
Your browser doesn’t support HTML5