Naira ta samu farfadowa a jiya tun faduwar da ta yi bayan dakatar da Sanusi Lamido

Naira ta samu farfadowa a jiya talata, tun faduwar da ta yi bayan dakatar da Sanusi Lamido Sanusi a makon da ya gabata,duk da fargabar da akeyi ta hasashen faduwar darajar takardar kudin ta Najeriya.

Mai rikon mukamin gwamna a babban bankin Najeriya, Sarah Alade, ta yi alkawarin ci gaba da manufar sarrafa kudade ta bankin duk da dakatar da gwamnan da akayi, ta kara da cewa babu wani shiri na rage darajar Naira.

Ta ce babban bankin zai cigaba da kokarin ganin cewa darajar kudin ta kasance cikin huruminta.

Wata masaniyar tattalin arziki a kamfanin hada-hadar kudade da ake kira Renaissance Capital, Yvonne Mhango, ta ce za'a iya daidaita farashin dalar Amurka akan Naira 170 abinda zaisa farashin kayayyaki ya haura sama.