Najeriya Itace Ta 53 A Jerin Sunayen Da FIFA Ta Fitar

Nigeria soccer fans celebrate after Nigeria's Sunday Mba scored a goal against Burkina Faso during their African Cup of Nations final match in Lagos, Nigeria, Sunday, Feb. 10, 2013. Nigeria erupted in celebrations after their Super Eagles won the Africa

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta zauna daram kan matsayin ta na 53 a jerin sunayen kasashe da FIFA ta fitar wanda suka fi gara tamaula, wanda aka fitar Alhamis 3 ga watan Satumba.

Zakarun wasan nahiyar Afirkan na shekara ta 2013, sun sami matsawa har gurbi hudu daga inda suke a watan Agusta. Sun kuma kasance ‘kasa ta tara a nahiyar Afirka, wanda kasashe kamar su Algeria (19) da Cote d’Ivore (21) da Ghana (27) da Tunusia (34) da Senegal (39) da Cameroon (42).

Abokiyar karawar su ta ranar Asabar a wasan neman samun guri a gasar cin kofin nahiyar Afirka, Tanzania wadda tazo lamba 140 a jerin sunayen da FIFA ta fitar, kuma ta 41 a Afirka.