A ci gaba da gasar Premier League ta Najeriya, kungiyar Eyimba ta doke Dolphins da ci 2-0 a birnin Aba, wanda ya hakan ya basu damar ci gaba da kasancewa a saman teburin gasar da maki hudu, yayin da gasar ta shiga mako na 29.
‘Yan wasa Andrew Abalogu da Ifeanyi Anaemena ne suka zirawa Eyimba kwallayenta cikin mintina na 64 da 74, wanda hakan ya basu damar mallakar maki ukun wannan karawa.
Yanzu Eyimba ba da maki 55 a wasannin 29 da ta buga.
A daya bangaren kuma, Warri Wolves ta doke Kwara da ci 3-0 a Warri.
Zakarun gasar Kano Pillars sun lallasa Abia Warriors suma da ci 3-0, yayin da Sunshine Stars ta sha kashi a hanun Nasarawa United da ci 3-2 a birnin Akure.
Wikki Tourist kuwa ta yi kunne doki ne da da ci 1-1 da Lobi Stars.
Sharks ta lallasa Ifeanyi Ubah da ci 1 mai ban haushi kana Enugu Rangers ta doke shooting starsa da ci 2-1.
A karshe Bayelsa kuwa ta lallasa El kanemi Warriors ne da ci 4-1 yayin da Akwa United ta doke Heartland da ci daya da banza.