Najeriya za ta Kara da Australia a Gasar Cin Kofin Duniya FIFA U.17

Kocin Super Eagles, Sunday Oliseh ya jinjinawa ‘yan wasan kasar na cikin gida, bayan da suka samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika.

‘Yan wasan sun samu wannan damar ne bayan da suka tashi canjaras da ‘yan wasan Burkina Faso a ranar Lahadin da ta gabata.

A wasan da bangarorin biyu suka buga a farko, Super Eagles ta doke Burkina faso da ci 2-0 a Port Hacourt.

Oliseh wanda yanzu haka yake hutun dole bayan da likitoci suka bashi shawara ya yi hakan, ya bayyana jin dadinsa a shafinsa na Twitter, inda ya nuna godiyarsa ga Allah da ‘yan wasan na Najeriya suka sami shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika wacce za a yi badi bayan da suka sami jumullar kwallaye biyu a wasanninsu da Burkina Faso.

Shekaru biyu da suka gabata Najeriya ta lashe kyautar tagulla a Afrika ta Kudu shekarar 2013.

Za a fara gasar ce a watan Janairun shekarar 2016 a kasar Rwanda.

A daya bangren kuma tawagar ‘yan wasan Najeriya za ta kara da takwararta ta Australia a rukunin ‘yan 16 a ci gaba da gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 da ake yi a Chile.

‘Yan wasan na Najeriya da ke samun jagorancin Emmanuel Amunike sun kasance na farko a rukininsu na A da maki shida, yayin da Australia suka kasance a matsayi na uku a rukunin C.

Wanda ya samu nasara wannan karawa zai shiga zagayen kwata final domin karawa da kasar da ta samu nasara a wasan da za a buga tsakanin Brazil da New Zealand.