WASHINGTON D.C —
A yayin da aka shiga rana ta hudu cikin a watan Ramadana, a yau Dandalin VOA ya sami zantawa da wani masani a harkar abinci a Jami’ar Bayero ta Kano Mal Balarabe Bilyaminu Ismail.
Malamin ya bayyana mana ire-iren nau’in abincin da mai azumi ya kamata ya ci a wannan wata bayan an sha ruwa don gujewa rudewar ciki ko amai da gudawa da sauran cututtukan da yawanci kan takurawa jama'a a lokacin da suke cigaba da aiwatar da ayyukan ibada a wannan wata na ramadana.
Malam Balarabe Bilyaminu ya kara da cewa tsabatace abincin shi kanshi na da matukar amfani domin kuwa rashin tsabta na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rudewar ciki.
Ku biyu domin jin cikakkiyar hirar.