Gobe Alhamis 31 gawatan Agusta na shekara 2017, za'a rufe hada hadar saye da sayarwar, 'yan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar 2017.
Chelsea ta maida yawunta kan sayen dan wasan tsakiya na Arsenal, Alec Oxlade Chemberlian, bayan sun cimma yarjejeniya da kungiyarsa ta Arsenal, akan kudi sama da fam miliyan £40.
Sai dai yanzu dan wasan yace ya canza ra'ayinsa na Komawa Chelsea bisa dalilansa na ganin kungiyar ta Chelsea zata yi amfani dashi ne a matsayin dan wasan gefe ba na tsakiya ba.
Manchester City ta ce zata ba da dan wasanta Raheem Sterling, da wasu Karin kudi ga kungiyar Arsenal domin ta mallaki dan wasan gabanta Alex Sanchez.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bukaci Manchester united da ta sayi Gareth Bale, inda a kwanakin baya Manchester, ta taya dan wasan har fam miliyan £90, shi kuwa Mai horas da 'yan wasa Zidane, ya ce ba na sayarwa bane.
Chelsea tana gab da sayen dan wasan tsakiya na Leicester City, Danny Drinkwater, akan kudi fam miliyan £40.
Tsohon dan wasan gaba na Barcelona, Neymar, ya shawarci takwaransa Philippe Coutinho, da karya kuskura ya Koma kungiyar Barcelona, daga Liverpool.
Neymar dai ya bar Barcelona ne zuwa kungiyar PSG ta kasar faransa a bana, akan zunzurutun kudi har yuro miliyan €222 inda ya zamo dan wasa mafi tsada a duniya bangaren tamola,
Sai dai bayan barinsa kungiyar ta Barcelona, ana ta samun takun saka tsakanin dan wasan da tsohowar kulob dinsa inda ko wannensu tsakanin Neymar da Barcelona ke cewar zai shigar da kara bisa cewar an cutar dashi a wasu hakkin kudade.
Your browser doesn’t support HTML5