Neymar Buri Ya Cika Na Kwallaye 100

Neymar

Barcelona ta doke Granada da kwallaye hudu da daya (4-1) a wasan da suka yi a ci gaba da gasar La-Liga na shekara 2017, dake gudana.

A karshen wasan Neymar ya sami sakamako mai kyau inda ya samu nasarar jefa kwallonsa na dari (100) a raga, wanda ya bashi damar cika burinsa.

A yanzu Neymar dan wasan gaba na Barcelona ya bi sahun irinsu Lionel Messi, Luis Suarez, Samuel Eto’o da Rivaldo, na kasancewa sunan sa ya shiga cikin jerin sunayen ‘yan wasan kwallon kafa da suka yi fice suka kuma taka rawar ganin a faggen ta mola.

Kafin ya kai wannan matsayin na jefa kwallaye dari a raga sai da ya buga wasani dari da saba’in da bakwai (177), ya kuma kasance dan kasar Brazil na uku da ya sami shiga cikin jerin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da suka jefa kwallaye dari (100) a raga baya Rivaldo da Evaristo ‘yan kasar Brazil.

Shekara da yafi jefa kwallaye a raga shine shekara 2014/2015 inda ya jefa kwallaye talatin da tara (39) cikin raga, a lokacin yana Catalans karkashen Luis Enrique.

Your browser doesn’t support HTML5

Neymar Buri Ya Cika Na Kwallaye 100 - 1'25"