Nishadi Tare da Baby-nice Ta Ce Basu Mara Mata Baya ba

Asma'u Sadiq {Baby Nice}

A shirinmu na nishadi a yau dandali ya samu bakwanci wata mawakiya Asmau Sadiq wacce aka fi sani da Baby-nice.

Baby-nice dai ta ce ta taso ne da son harkar fim bayan da ta nemi shawarar iyayenta ko da yake basu mara mata baya ba, kuma da yake a lokacin ta na zuwa wata makaranta ta Kwamfuta kuma a kusa da makaranta akwai wani studio da mawaka da yan fim ke zuwa ganin tana da shawarar fim idan aka tashi daga makaranta sai ta je wajen tana kallonsu.

Da tafiya tayi tafiya sai ta fara aiki a studio a matsayin sakatariya, da kadan da kadan sai ta fara rubuta waka har ta kai da ta fara rairawa.

A wajen da take aiki a studio tana da wani abokin da ya ja ta ga harkar fim inda ta fito a wasu fina-finai da suka hadar da Rashin Uwa, Matattakala ,sako na masoya da sauransu.

A fannin tsegumi kuwa gwamnati jihar kano ta ce zata fito da wata kasuwa da zasu dinga sayar da fina-finai kadai.

Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar da Asmau Sadiq wacce aka fi sani da baby-nice.