Nishadi Da Ghali Landmark Furodusa Kuma Marubuci

Na samu horon yadda ake hada sauti tare da gyaran murya kamar yadda wani furodusa kuma mawaki a jihar Lagos, ke bayyanwa wakiliyar Dandalin VOA a Lagos.

Ghali Landmark furodusa kuma marubuci ne a hannu guda, kuma mawaki na wakokin Hausa hip hop, wanda ya shafe shekura ya na wannan masana’anta.

Ya ce ya faro waka ne a lokacin suna tare da wasu abokansa a kungiya, ko da yake ya ce ya samu horo a harkar waka, wanda har ta kai shi ga zuwa kasar Jamus, inda ya hadu da wani abokinsa wanda ya koya masa yadda ake hada sauti.

Ghali Landmark ya ce ya zuwa yanzu dai ya reni wasu mawaka masu tasowa, daga cikin wadanda suka taso ta wajensa ciki har da fitattacen mawakin nan dan Lagos wato B Merry.

Ya ce yana hada sauti yana kuma gyara murya ta fita yadda mawaki ke so, ya kuma ce waka a Lagos ba kamar yadda ake yinta a Arewacin Najeriya ba ne.

Ya na mai cewa dole sai an hada da hakuri da juriya kafin mutum ya cimma gacci sannan dole sai an hada da talla da ziyartar gidajen rediyo domin su tallata hajjar su.

A bangaren aiki a studio kuwa, Landmark ya ce a mafi yawan lokuta yakan fuskanci matsaloli na rashin biyan kudi ga wasu daga cikin mawaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Nishadi Da Ghali Landmark Furodusa Kuma Marubuci