Nishadi Da Mawakin Hip-Hip Auwal Kwamanda

Awal Kwamanda

Auwal Kwamanda ya fara waka ne tun yana makarantar sakandare, inda ya fara rubuta waka a lokutan da ba a darasi.

Auwal Boy Commander, wanda ya fi kwarewa a fannin hip-hop, ya ce yana isar da sakonnin da suka shafi zaman lafiya da hadin kai da kuma matsalolin rikce-rikicen da ke ciwa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, baya ga haka kuma ga matsaloli na soyayya da zamantakewa.

Kamar kowanne mawaki, kwamanda Auwal ya fuskanci wasu matsaloli mussamam ma daga wajen mahaifinsa, inda ya ke ce masa waka, ba sana’a ce ba da zai ba shi damar aiki ba. A haka dai ya ci gaba a boye har ya fara.

Baya ga wakoki da yake yi, ya ce yana fitowa a wasu fina-finan Hausa, wanda ya ke yi a jihar Lagos. Daga cikin fina-finansa akwai "Bakon Lages", sai kuma "Ba kiyiwa ba biyan bukata"

Ya ce babban burinsa a harka ta waka itace ya zama babban mawaki da aka san shi a sassan duniya da dama. Ya ce waka sana’a ce da take kawo kudi da yawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Auwal Boy Commander