Nishadi Tare Da Salmanu Mazika

Salman Mazika

Kamar yadda muka saba hira da mawaka da jarumai domin jin yadda abubuwa daban daban ke faruwa a cikin wannan sana'a, dandalin voa ya sami zantawa da Salmanu Mazika wani mawaki da ya ce iya saninsa a wannan rayuwa, ya fara waka ne daga lokacin da ya fara wayau,

kuma yana wakokin nanaye da na siyasa har da da wakoki fina-finai ya ce a yanzu dai zai fi mai da hankalinsa ne a wajen yi wa Manzon Allah kasidoji har iya tsawon rayuwansa.
Mazika ya ce koda yake zai cigaba da yin wakokni biki ko suna ko na fina-finai amma fa ba zai yi wa wani waka ba.

Kamar yadda matashin ya bayyana, basirar raira waka wata baiwa ce adaga Allah kuma yakan tsara wakokin sa ba tare da taimakon wasu ba, ta dalilin haka ne matashin ya fara rerawa dandalinvoa waka a yayin da wakiliyar dandalin voa Baraka Bashir ke gudanar da wanna hira da shi.

Ga cikakkiyar hirar