Ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sudan ta Kudu ya taimaka wa wasu ‘yan kasar har su sama da 40 dake da takardun izinin zama ‘yan kasashe biyu, Sudan ta Kudu, da Amurka, damar fita kasar Sudan ta Kudun, a karshen satin da ya shige.
Wadannan mutanen dai dukkan su, suna zaune a sansanin ‘yan gudun hijirar farar hula na Juba, wanda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya tun a cikin watan Juli, lokacin da fada ya barke a babban birnin kasar. Ranar alhamis din nan mai zuwa ne idan, Allah ya yakai mu ake sa ran shugaba Donald Trump, zai karbi bakuncin shugaban kasar China XI Jinping.
Tun lokacin da fadan ya barke ne suka so fita amma suna tsoron yin haka domin dangantakar su da tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Macher, da ake takon saka tsakanin sa da shugaba Salvar Kirr.
Mutanen wadanda su 42 ne maza da mata da yara, sun samu damar arcewa ne a cikin wani jirgin haya wanda zai fara kai su Cyprus, a ranar asabar din data gabata.
Jakadan Amurka da ke kasar ta Sudan ta Kudu, Molly Phee, shine ya fara agaza wa wadannan mutanen, lokacin da ya samu labarin cewa akwai wasu ‘yan Amurka dake sansanin kuma suna neman barin wurin domin komawa Amurka amma lamarin yaci tura, daga lokacin ne ya fara shirya yadda zai agaza musu domin barin kasar baki daya.
Jakada Phee, yace lokacin da suka nemi tafiyar da farko, ba a kammala shirya takardun tafiyar su ba, sai da ya tabbata komi ya hadu kafin su wuce, yace kuma ofishin jakadancin yayi aiki kafada da kafada ne da wasu ma’aikatun gwamnati guda biyar.
Wasu daga cikin mutanen dai sun jima cikin kasar wasu kuma sun dawo ne a cikin shekarar 2015 lokacin da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya , amma kuma yarjejeniyar bata yi karko ba.