Ra'ayoyi Akan Sa Hannun Maza A Ayyukan Gida

Kamar yadda muka saba jin ra'ayoyin jama'a daban daban musamman a kan halaiya da zamantakewar rayuwa jama'a, a yau dandalin voa ya nemi jin tabakin jama'a ne musamman akan tasirin hada hannu tsakanin miji da mata wajan gudanar da ayyukan gida kama daga shara, da wanki, da guga, da dafa abinci, yi wa yara wanka da sauran su.

Maza dai musamman a al'umar Hausawa basu cika sa hannu a ayyuka makamantan wadan nan ba, am fi sanin su ne da zuwa nema, wato aiki ko gona ko kasuwa da sauran wuraren da suka saba zuwa neman abinci.

Koda shike zamani ya canza, amma kamar yadda wasu suka bayyana man na su ra'ayin, taimaka wa mata da ayyukan gida na da matukar amfani wajan kara kulla dangon zumunci da kaunar juna da kuma samar da iyali masu nagari.

Koda shike ba'a taru an zama daya ba, wasu daga ciki sun bayyana cewa babu yadda za'ayi suje neman abinci sa'an nan su dawo gida su kama aiki, a cewar su, mata aka sani da ayyukan gida.

Ga cikakkiyar hirar.