Wani babban jigo, a Kannywood Peter Andrew, ya ce kalubalen da ke ci wa harkar fina-finai tuwo a kwarya bai wuce yadda wasu daga cikin daraktoci ke yi wa harkar editin rikon sakainar kashi ba, ta yadda a mafi yawan lokutan sukan bar aikin editin ga masu editin kadai.
Ya ce a ka’ida darakta kamata yayi ya zauna tare da mai aikin editin domin ya nuna yadda yake so aikin nasa ya kasance, sakamakon rashin lokacin da burin yin wasu ayyukan yakan sa daraktoci kan bar aikin a hannu edita wanda daga baya haifar da da mai ido.
Ya kara da cewa daga cikin matsalolin da ke ciwo wa masana’antar tuwo a kwarya akwai rashin nuna sahihanci ko gaskiyar lamari a fina-finai Kannywood, domin a mafi yawan lokutan gundarin labarai da Kannywood ke fitar wa baya nuna kanshin gaskiyar lamarin.
A ta bakinsa sa ya ce alal misali idan matar mutum tana cikin tsananin rashin lafiya a fina-finan baya nuna damuwa ko tausayi wajen kai ta asibiti ko akasin hakan .
Peter ya kara da cewa idan aka yi wasu ‘yan gyare gyare da sa idon da ya kamata wuri harkar fina finai to tabbaci hakika za a baiwa marada kunya.
Your browser doesn’t support HTML5