Real Madrid Ta Matsa Kaimi Kan David de Gea

Mai tsaron raga na kungiyar Manchester united David de Gea, yana jira a kan yarjejeniyar sabunta Kwantirakin sa a kungiyar, duk da cewar dan wasan dan kasar Spain mai shekaru 27 da haihuwa yana da watanni 16 da suka rage masa a kulob din.

Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta kasar Spain ta matsa kaimi wajan ganin sun dauko dan wasan a karshen kakar wasan bana.

Wakilin dan wasan tsakiya na Liverpool Emre Can's ya dakartar da duk wata tattaunawa da za'ayi da dan wasan kan matsayin sa a kulob din,
Ita kuwa Liverpool ta ce tana bukatar dauko dan wasan tsakiya na Barcelona Ivan Rakitic.

Your browser doesn’t support HTML5

Real Madrid Ta Matsa Kaimi Kan David de Gea