Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, ya bada tabbacin cewa dan wasan gabansa na gefe Gareth Bale, dan kasar Wales, ya samu rauni a kafarsa.
Gareth Bale ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta Real Madrid, tayi da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, na kasar Jamus, a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a satin da ya gabata inda Real Madrid, tabi Borussia Dortmund har gida ta doke ta 3-1.
Sakamakon wannan rauni da yaji Gareth Bale mai shekaru 28 da haihuwa zai tafi jinyar sati hudu kafin ya dawo fili da taka leda.
Don haka dan wasan ba zai samu damar fafatawa a wasan da kungiyarsa ta Real Madrid, zatayi da Tottenham, na kasar Ingila, ba a wasan cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) zagaye na uku a wasan rukuni.
Haka kuma Bale, bazai samu damar buga wasanni biyu da kasarsa ta Wales, za tayi da Kasar Georgia, da kuma kasar Ireland ba a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekara 2018 da za'ayi a Rasha.
Your browser doesn’t support HTML5