Ribar Kamfanin Sadarwar Salula MTN ta Karu Fiye da Kiyasin Farko - 05/03/14

MTN

Akasarin ribar ta fito ne daga Najeriya, inda masu amfani da layukan MTN suka karu da kashi 20 cikin 100.

Kamfanin sadarwar salula na MTN, wanda shine mafi girma a Afirka, ya samu ribar kashi ashiri da bakwai cikin dari, fiye da abinda yayi kiyasi tun farko.

Yawan masu layukan salula na MTN ya karu da kimanin kashi goma cikin dari,inda yanuna cewa masu amfani da MTN yanzu sun kai fiye da miliyan dari biyu da bakwai, inda kashi ashirin daga cikin dari na karin yazo ne daga Najeriya kasar da tafi kowace yawan masu amfani da layukan wayar na MTN a duniya.

A wani labarin kuma Bankin First Rand, wanda shine na biyu wajen bada rance na Afirka ta kudu,yace zai bude harkar banki a Najeriya domin cin gajiyar bunkasar tatalin arzikin kasar.

Shugaban,bankin Sizwe Nxasana ne ya furta haka ta wayar tarho,yace tuni bankin ya fara hurda da yan Najeriya.

Shugaban bankin ya kara da cewa har yanzu suna sa rai wajen siyan bankin Mainstreet ko kuma bankin Keystone a Najeriya tunda yake harka a Afirka ta kudu ya ja baya.