Rahotanni a kawanakin da suka gabata sun bayyana yadda babban bankin Najeriya CBN ke ta shirye shiyen bullo da wasu sababbin manufofi wadanda a cewar sa, zasu taimaka wajan bunkasa ta tattalin arzikin kasa.
A yayin da gwamnan babban bankin Mr Amefiele ke jawabi akan sababbin manufofin bankin a birnin Abuja, gwamnan ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan sun hada da farfado da darajar Naira gwargwadon yadda kasuwa ta kaya.
A cewar daraktan yada labarai na bankin, babban makasudin yin hakan shine jama’a da dama na korafin cewa manufofin bankin sunsa basa iya samun kudaden musaya saboda haka ne yasa suka gay a dace su ba kasuwa damar daidaita al’amurra ta hanyar barin Naira ta samawa kanta daraja a kasuwa.
A cewar tsohon babban manajan daraktan bankin Jaiz na farko a Najeriya Alhaji Muhammadu Mustapha wannan tsari ne mai kyau, domin kuwa a cewar sa hada hadar kasuwanci zata fi yadda take a da, kuma ‘yan kasuwa da suka boye dala a wannan lokacinne zasu fara fito da ita.
Ya kara da cewa da zarar an fara samun dala a kasuwanni duk wahalar da ake fuskanta na wahalar samun canji da sauran su, zasu kau domin kuwa matasa zasu sai aiyukan yi saboda kamfanoni zasu bude, kuma kasuwanni da masana’antu zasu sami hanyoyin bunkasa abubuwan da suke yi. Saboda haka lallai za’a sami gyara.
Your browser doesn’t support HTML5