Sabuwar Fasahar Kamfanin Amazon Ta Saukaka Harkokin Saye Da Sayarwa

Shafin amazon.com ya kaddamar da wata sabuwar manhaja mai suna Spark da zata baiwa masu amfani da shafin damar bajekolin hajarsu su kuma su sayi kayayyaki akan dandalin.

Wannan shine karon farko da Amazon, ya karkata zuwa kafofin sada zumunta da harkokin kasuwancin sa.

Manhajar Spark, wadda yanzu haka mutanen da sukayi rijista da amazon prime zasu iya amfani da ita, na karawa mutane kwarin gwiwar kafe hotuna da bidiyo, kamar yadda ake a fitattun kafafen sada zumunta irinsu Instagram da Pinterest.

A cewar mai magana da yawun kamfanin Amazon, “Mun kirkiri manhajar Spark ne domin ta taimakawa masu sayayya samo kayayyaki cikin sauki.”

Da yawa daga cikin masu sayayya a shafin Amazon, sun kafe a kafofin sada zumunta suna bayyana farin cikinsu game da yunkurin kamfanin na samar da harkokin kasuwanci cikin salon kafafen sada zumunta na zamani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabuwar Fasahar Kamfanin Amazon Ta Saukaka Harkokin Saye Da Sayarwa