Shirin nishadi na wannan mako ya samu bakwanci mai shirya fina finai wato {Producer} ,a yanzu Habibu Yaro Haruna ,wanda ya fara harakar fim shekaru goma sha biyar da suka wuce , ya dai fara ne daga matakin jarumi ,inda ya fito a fim din ‘Ki yarda da ni’ daga bisana a wasu fina-finan Mandawarin enterprise sannan ya zamo make-up artist sai set designer sannan a karshe ya tsinci kansa a matsayin mai shirya fina finai {producer.}
Habibu Yaro ya ce abinda ya sa ya tsinci kansa a harkar fim a matakin producer dai a cewarsa harkar fim harkace da ake samun suna , komai na rayuwa sannan harkar ce ta komai da ruwanka wato abinda ake kira da turanci Team.
Ko da ya ke ya koka da matsalar satar fasaha da masa’anatar ke fuskanta , inda ya ke cewa har sai gwamnati ta shigo ciki domin magance wannan matsalar.
A fannin tsegumi kuwa a makon da muka yi bankwana da ita ne Shugaban hukumar tace fina-finai wato Afakallahu ya gana da masu daukar hoto wato (DOP) na masana’antar.