WASHINGTON D.C —
A yau mun tattauna ne da matasa inda suka bayyana mana ra'ayoyin su akan dalilan da ke sa wasu 'yan mata ke makale ma wasu samari duk da irin wulakancin da suke fuskanta daga gare su.
Koda shike ba'a taru an zama daya ba a cewar wani daga cikin matasan, amma aganin shi kwadayi ne ke sa yawancin 'yan mata su makalewa wasu samari masu muzguna masu.
Ya bada misalin yadda wata budurwa ke kai masa dinkin kaya kuma a kyauta yake yi mata, amma daga bisani sai ya gano cewar babu son gaskiya a tsakanin su illa morar sa da take yi domin yi mata dinki a kyauta.