Cikin ‘yan makwanni masu zuwa ake sa ran kamfanin Samsung zai kaddamar da sabuwar wayarsa ta Samsung Galaxy S9.
Ita dai wayar Galaxy S9 ita ce sabuwar wayar da kamfanin Samsung zai fitar daga jerin wayoyinsa, wayar da aka kayata da wasu sabuwar fasaha.
Samsung ya aika da katin gayyatar wani taro da zai yi ranar 25 ga watan Fabarairu, a babban taron wayoyin hannu na duniya da za a yi birnin Barcelona, domin bayyana sabuwar wayar Galaxy S9 kayatacciyar wayar da ya kera wadda ake ganin zata kara da sabuwar wayar iPhone X.
A shekarar da ta gabata, wayar Samsung Galaxy S8 ta kawo ci gaba sosai ga kamfanin. Ana sa ran sabuwar wayar da za a fitar zata kasance tana da kyamarar ‘daukar hoto har biyu, za kuma a ‘kara mata karfin sarrafawa.
Yanzu haka dai mutane ba zasu iya biyan kudinsu su jira lokacin fitowar wayar ba tukunna, har sai kamfanin ya kaddamar da sa ranar da wayar zata fito ga jama’a.
Your browser doesn’t support HTML5