Sana'ar Sakar Huluna da Rigunan Sanyi.

Adere da aka saka a Agayawa jihar Katsina Nigeria

Wata mata mai Suna Malama Abu, wadda ke sana’ar yin saka tace, a rana tanayin rigunan sanyi da huluna fiye da goma, kuma tayi kira ga matasa da su tashi tsaye su dogara da kansu domin rage zaman banza.

Wannan mata dai mai suna Abu Audu, tace tana sana’ar yin saka irin ta inji wadda akeyin riguna da hulunan sanyi dadai sauransu. Kuma tace ta gaji wannan sana’ar ne daga gidansu tun tasowar ta, wanda yanzu haka a rana tana saka riguna sama da ashirin, huluna kuma tanayin dayawa a dalilin sanyi akeyi. Malama Abu ta gayamana cewar mutane da dama na zuwa gida domin su sayi kayayyakinta, a kwai kuma wadanda take baywa kayan domin kaisu kasuwa a sayar.

Tace kuma tana koyawa ‘yan uwanta mata wannan sana’a, domin a kwai mata dayawa zasuzo suce suna son a koya musu musammamma lokacin sanyi. Ta dai koya wannan sana’a tata ga mata dayawa domin suma su anfana.

Kiranta ga matasa shine su rage zaman banza, su tashi su dogara da kansu ba sai sun zauna komai sai anyi musu ba, saboda idan suna sana’a komai zasu iyayi harma zasu iya taimakawa wadansu. Malama Abu, bada wannan sana’a kadai ta dogara ba tana yin aikin gwamnati.

Your browser doesn’t support HTML5

Sana'ar Saka 0'59"