WASHINGTON, DC —
Daya ga watan Fabrairu, kowace shekara ne ake bukin ranar sanya hijabi, wanda ya samo asali daga wata mazauniyar New York, a kasar Amurka, mai suna Nazma Khan.
Taken ranar na bana dai shine, wayar da kan al’uma, sanin manene hijabi, zaman lafiya duniya.
Ita ta fara wayarwa matan duniya kai ta hanyar sadarwar yanar gizo, wato {Internet} wanda hakan ya ja hankalin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba a kasashen duniya.
An fara bukin wannan ranar ce a shekara 2013, don jan hankalin matan duniya, wajen sujurta jikinsu da kuma kwadaita masu sa hijabi, koda sau daya ne domin gani yadda girmama mace yake a Musulunci.
Your browser doesn’t support HTML5