Sarkin Kano ya Karbi Sandar Mulki

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu

A yau ne aka rantsar da mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, wanda Limamin Kano Farfesa, Muhammad Zaharaddeen, ya gudanar.

Bayan rantsuwar sai kuma bada kayan mulkin gidan Dabo, a bisa al’ada, wanda Galadiman Kano, daya daga cikin masu zabar sarki a majalisar masarautar Kano, Malam yusuf Nabahani, ya mikawa Sarkin wadanda suka hada da Wukar Dabo, da rawani da kwari da baka da alkebba.

Inda ba’a manta ba bara, a watar Yuni ne Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya zama Sarkin Kano, na hamsin da bakwai, biyo bayan rasuwar marigayi Sarki Ado Bayero, Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, shine ya mika sandar ga sabon sarkin na Kano.

Baki daga ciki da wajen Najeriya, ne suka halarci taron wadanda suka hada da jakadar Amurka, a nan Najeriya, Mr James Entwistle, da tsofaffin shuwagabanin Najeriya, wadanda suka hada da Janar Yakubu Gowon da janar Muhammadu Buhari.

Mai martaba Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, da sauran sarakuna, daga arewa da kudancin Najeriya, sun halarci bikin.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kano - 3'24"