Tsohon shahararren dan kwallon kasar Brazil Pele, zai kai ziyarar kwanaki biyu a Najeriya karkashin wani shirin karfafa matasa na nahiyar Afirka, daga ranar 11, zuwa 12 ga wannan wata na agusta.
Pele ya taba lashe kofin duniya na kwallon kafa har sau uku da kasar sa Brazil, zai shugabanci wani wasan kwallon kafa na matasa da za’a gudanar a Ikoyi dake jihar Legas, sa’annan ya jagoranci wani taro da hukumomin Najeriya.
Zai kuma gana da matasa masoya kwallon kafa da kuma iyayensu daga jihohin kasar daban daban, zai kuma halarci wani bikin gala tare da wasu shahararrun ‘yan kwallon nahiyar Afirka.
A wajan bikin za’a kaddamar da wata gidauniya domin tallafawa wasu cibiyoyin koyar da kwallon kafa a Najeriya. Wannan ziyara ta Pele zata kasance ta biyu a Najeriya, bayan ziyararsa ta farko a shekarar 1967.
An bayyana sunan Abdul’jabbar Sani a matsayin sabon kaftin din ‘yan wasan kwallon kafa masu kasa da shekaru goma sha bakwai U-17, Golden Eaglets a dai dai lokacin da ya rage kwanaki kalilan su fafata da takwarorin sun a jamhuriyar Nijar, a wasan neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta ‘yan kasa da shekaru goma sha bakwai.
Your browser doesn’t support HTML5