Shan Sukari na iya Haifar da Cutar Kiba

Obesity Risk

Hukumar kiwon lafiya ta duniya da ake kira WHO a takaice, ta yi kashedin cewa yawan shan sukari na iya haifar da cutar muguwar kiba, lalacewar hakora, da kuma wasu cututtukan.

Cibiyar ta MDD, ta fidda wasu sabbin bayanai inda ta ba matasa da yara shawarar su rage adadin sukarin da suke sha kullum.

Hukumar kuma ta fadi cewa yawan masu cutar muguwar kiba ya karu sosai tun Aluf dari tara da tamanin.