Bankin tare da hadin kan gwamnatin jihar Kano su na samar da jari ga kananan masu sana'o'i kamar wannan mace mai sayar da tuwo a birnin Kano
WASHINGTON, DC —
Babban bankin Najeriya tare da hadin kan gwamnatin Jihar Kano, sun bullo da wasu shirye-shirye na tallafawa masu kananan masana'antu da ma mata masu sana'o'in hannu ta yadda zasu samu jarin gudanar da sana'o'in nasu.
Domin cimma wannan guerin ne ya sa aka bude kananan bankuna na taimakawa masu kananan sana'o'in.
Ana gudanar da bita ga irin wadannan masu kananan sana'o'i kan yadda zasu iya cin gajiyar wannan tallafi na bankuna, da kuma yadda zasu iya kula da irin wadannan sana'o'i nasu.
Wakiliyarmu Baraka Bashir ta tattauna da Hajiya Hauwa Mai Tuwo wadda ke sayarda abinci a Malam kato Square a Kano.

Your browser doesn’t support HTML5