WASHINGTON, DC —
Shugaba Buhari, ya ja kunnan matasa dangane da ta'ammali da miyagun kwayoyi yana mai cewa duk wanda aka kama to lalle doka zata yi aiki ta kuma babu afuwa, ya ce Gwamnati na tattaunawa da makwabtan kasashe domin neman hanyoyin da za’a bullo wa batun.
Shugaban yayi wannan gargadin ne a hira da muryar Amurka a lokacin da ya yi tattaki zuwa birnin New York, ta kasar amurka inda ya halarci taron Majalisar dinkin duniya.
Ya kuma umarci iyaye dasu dasu taimaka da bayanai na duk inda sauka san ana sayarda miyagun kwayoyi da kuma sa idon akan ‘ya’yan su dan sanin irin abokan da ‘ya’yan su ke abota dasu, gyara kayan ka bai zamo sauke mu raba ba domin hannu daya baya daukar jinka.