Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sake Gabatar Da Yaki Da Rashin Da'a

A jiya litini, yaki da rashin da’a a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ya dauki wani sabaon salo, inda shugaban ya sake gabatar da sabuwar rundunar jami’an yaki da rashin da’a da aka fi sani da War Against Indiscipline, a birnin tarayya Abuja.

Da yake jawabin bude ayyukan hukumar a karkashin gwamnati mai ci yanzu, shugaba Muhammadun Buhari ya bayyana cewa jami’an zasu taimaka wajan tabbatar magance rashin tsaro a tsakanin al’umma, da tashe tashen hankula, da yawan satar mutane domin kudin fansa, da sauran miyagun ayyuka makamantan su.

A yayin da yake Magana lokacin bukin gabatar da jami’an, babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a “National orientation Agency” Dr Garba Abari ya ce gwamnatin ta yanzu ta yanke hukuncin sake kaddamar da ayyukan yaki da rashin da’a domin inganta yakin da take da rashin da’a da kuma cin hanci da rashawa.

Kamar yadda mujallar Daily Post ta wallafa, shugaban ya ce ya tuna da cewa a karkashin mulkin soji na Janar Muhammadu Buhari daga shekarar 1984 zuwa 1985 ne aka fara kaddamar da wannan shiri na yaki da rashin da’a da cin hanci da rashawa domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya kasance mai kiyaye dokokin kasa da halaye nagari.

Shirin ya sami karbuwa kwarai kamar yadda kowane dan Najeriya a lokacin ya tilasta kanshi domin aiwatar da ayyuka da halaye nigari, rayuwar da ta dauki lokaci kafin ta kau duk da cewa yabar kargar mulki a lokacin.

Shirin yaki da rashin da’a na adawa da ayyukan da suka hada da cin zarafin dan’adam dake da nasaba da ‘yanci, da yin adalci, da daidaito tsakanin al’umma bakidaya.