Siyasar Tone-Tone Ta Kunno Kai a Najeriya

Najeriya Zaben 2015 Buhari da Jonathan

Salon kamfe na tone-tone ya kunno kai a wannan karon a siyasar Najeriya, baya ga jam’iyyar PDP, ko shugaba Jonathan, dake cewa ko a zabi jam’iyyar PDP, a kara samun ci gaba ko kuma a kauce a maida hannun agogo baya.

Ita kuwa babbar jam’iyyar, adawa ta APC, na cewa zata kawo canji, dangane da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya, ke fuskanta.

A irin wannan kamfe na tone-tone har da dauko bayyanai Masamman ma da PDP, ke nuna janar Buhari, a matsayin mai tsattsauran ra’ayi, ka zalika a wannan karo ne jam’iyyar, mai mulki ta kawo batun takardun makarantar janar Buhari, da bata yi hakan ba a karo uku da yake takarar a baya.

Inda hukumar zaben, ta bakin mataimakin daraktan ta Nick Dazan, ta maida martini cewar idan wani yana da wani Magana ne daban akan janar Buhari, mutun yana iya zuwa kotu,domin mu mun gamsu saboda, a bisa ga doka idan jam’iyya, ta mika mana dan takara hakkin mune mu amshi dan takarar, tambaya a nan shine mutune zai iya kaiwa wannan matsayi batare da yayi sakandare ba.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP da APC - 2'50"