Southampton Ta Kori Kocinta Mauricio Pellegrino

A yayin da ya rage saura makonni takwas a kammala gasar Firimiya lig ta kasar Ingila, kungiyar kwallon Kafa ta Southampton, ta kori kocinta Mauricio Pellegrino.

Kungiyar ta ce ta sallame shi ne sakamakon rashin tabuka abin kirki a kungiyar musamman a gasar Firimiya lig.

Pellegrino dan shekaru 46 da haihuwa ya kama aiki a kungiyarne a watan yunin 2017 bayan ta Sallami kocinta Claude Puel, a sakamakon shima bai tabuka abin kirki ba.

Southampton, ta sami nasara a wasa daya ne kacal a cikin goma sha bakwai da ta yi a karkashin jagorancin Pellegrino, inda a ranar asabar da ta gabata Newcastle, ta lallasata da ci 3-0 a gasar Firimiya lig mako na 30.

A yanzu haka tana mataki na 17 da maki 28 a wasannin mako na 30 da ta buga na Firimiya lig. Kungiyar ta ce kafin ta yi wasanta da Wigan a ranar lahadi zata samo Kocin da zai cigaba da jagoranci kungiyar.

Your browser doesn’t support HTML5

Southampton Ta Kori Kocinta Mauricio Pellegrino