A yayin da matasa ke kokarin neman abokan soyayyar su, iyaye maza da mata kuma shawarwari suke bada wa musamman akan yadda 'ya'yan nasu yakamata su bi a hankali domin kaucewa kuskure.
Soyayyar zamanin yanzu ta banbanta da soyayyar da, abin la'akari anan kuwa shine, yadda samari da 'yan mata ke haduwa da juna a wurare daban daban har ma daga karshe soyayyar su kan habaka har ta kai su ga aure.
Kamar yadda wani magidanci ya bayyana, a zamanin su, yawanci iyaye ne ke hada su, a wani lokaci ma sai dai a fada wa budurwar ko saurayin cewar an yi masu miji ko mata kuma hakan zata kasance.
Zaku iya amincewa da irin wannan auren a yanzu?
Kamar yadda wasu daga cikin matasan suka bayyana ra'ayin su musamman dangane da irin abubuwan da za su iya daukar hankalin su har ma su fara son juna, zai iya zamowa da daure kai idan aka wayi gari mahaifa sun yanke hukuncin hada aure ba tare da sanin ma'auratan ba.
Ku same mu a shafin mu na facebook/dandalinvoa domin tafka muhawara.