Stephen Keshi Ya Ja Kunnen 'Yan Super Eagles

Kwach na ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, Stephen Keshi, ya ja kunnen ‘yan wasansa a kan su kara himma idan sun hadu domin shirin fara neman zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2017 a wata mai zuwa.

‘yan wasan na supre Eagles dai basu sami damar zuwa kare kofin a gasar ta bana da aka buga a kasar EG ba, saboda anyi waje rod da su.

A watan gobe na Yuni ne ‘yan Super Eagles din zasu fara gwagwarmayar neman gurbi a cikin gasar ta 2017 a karawar da zasu yi da kasashen Chadi da Tanzaniya.

Keshi yace wannan lokaci na damina a Najeriya, mawuyacin lokci ne na hada ‘yan wasa wuri guda a saboda wannan lokacin hutunsu ne. Amma ina son su kasance masu kwazo da himma inji shi.

Yace zai yi magana da dukkan ‘yan wasan da za’a gayyata a kan su kasance masu himma ga dukan burin dake gabansu, kuma zai tunatar da su irin bakin cikin da kungiyar ta shiga a watannin baya da kuma irin burin da ta sanya a gabanta yanzu.

A bayan Chadi da Tanzaniya, Najeriya zata gwabza da Masar a wannan rukuni nasu. Kungiyar da tazo ta daya , zata samu shiga gasar ta lashe kofin kasashen Afirka ta Gabon 2017. Sannan za a zabi wasu kungiyoyi guda biyu daga dukkan rukunonin wadanda sune suka fi yawan maki ko jefa kwallaye daga cikin wadanda suka zo na bibbiyu a rukunonin su.