Sun Hada Baki Da Yaro Domin Satar Mashin

Rudunar ‘yan Sandan jihar Osun, ta gurfanar da wasu matasa biyu a gaban kotun a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun abisa zargin satar mashin na hawa.

Matasan Wahab Maruf, mai shekaru ashirin da uku (23) da Adadeji Abiodun mai shekaru ashirin da takwas(28), na fuskantar laifufuka hudu ne da suka hada da sata da hada baki da kuma batanci.

Laifuffukan sun sabawa sashe na 516, 390(9) 430(2) da kuma 415 na kundin laifuffukan jihar Osun.

Dan Sanda mai gabatar da kara Saje Rasaki Abiodun ya fadawa kotu cewa wanda ake zargi ya hada baki da wani yaro mai shekaru goma sha hudu domin ya sace wani machin samfurin Bajaj, na wani mai suna Lateef Kolapo.

Wadanda ake zargi basu amsa laifinsu ba, kuma Lauya mai karesu Najite Okobie ya neni kotu da ta bada beli mai shara’a Fatima Sodamade ta bada belinsu akan kudi Naira duibu dari biyu (200,000) kowane da mutun daya mai tsayawa kowanensu, an kuma dage karar zuwa 31, ga watan janairu 2018.