Daruruwan daliban makarantun koyon sana’ar, hannu dake jamhuriyar Nijar Yau sun gudanar da wata zanga zangar lumana, abirini Yamai, daga bisani suka tarun a zauren wasanin gargajiya ko kuma dandalin fahimtar juna wanda yake daf da majalisar dokokin kasa.
Daliban na korafi ne kan tarin wasu matsaloli ciki harda rashin sami kudaden alwus alwas, a lokacin da suka ce kudi karatu ya tashi, a makarantu masu zaman kansu.
Dan daga cikin daliban wani Sule Muhammad Guruza, ya ce ya kai shekara daya daliban na tambayar Gwamnati kudadensu amma babu wani abinda Gwamnati tayi.
Yana mai cewa Gwamnati tayi kwance da kaya, shi yasa daliban suka fito yin zanga zanga domin nuna rashin jindadinsu.
Kungiyar hadakar daliban makarantun koyan sana’ar hannu na birnin Yamai, ce ta shirya wannan zanga zangar domin tayar da hukumomi daga barci a game da matsalolin da daliban suka kira dadaddu, kuma a cewar wani jigon kungiyar Muhammadu Sidi Ibrahim, zasu ci gaba da gwagwarmaya har sai sun ga abinda ya turewa Buzu nadi.
Your browser doesn’t support HTML5