Matasa Su Mayar Da Hankali Wajen Neman Illimi -Inji Fatima Muhammad

Fatima Muhammad – ta ce babban kalubalen da ta fuskanta a matsayinta ta mace da ta fara karatun na gaba da sakandare shine, bata sami kwas (Course) din da ta bukaci ta karanta ba, ta so ta zama Nas (Nurse), amma ta samu gurbin karatu a fannin ilimin koyarwa da harshen larabci, inda ta fuskanci gwagwarmaya da dama.

Ta ce ko da ta fara karatun ‘Education Arabic’ a shekarar farko duk kwasai-kwasan da ta dauka babu wanda tasamu nasara maimakon hakan ma sai ta ga ta samu F9 (Fail) a dukkanin kwas din da ta dauka, a shekara ta biyu ne ta maida hankali a cewar ta da kyar ta kammala karatunta na NCE.

kammalawar ta ke da wuya sai ta fara koyarwa, inda ta nemi gurbin karatu a jami’ar Bayero ta Kano inda ta samu ta karanta Education Hausa, a nan ne ta maida hankali ta kammala karatunta na digiri cikin sauki.

Ta ce a lokacin da take karatun ta na jami’a kalubalen da ta fuskanta shine na dadewa a makaranta kasancewar da aurenta ne ta shiga jami’a, mafi yawan karatun na kai ta dare kuma ko da ta gama ta cigaba da koyarwarta.

A koyarwa malama Fatima ta ce bata fuskanci wata matsala ba sakamakon ita malama ce tun da farko, a duk makarantar da ta tsinci kanta abinda take fara dubawa shine yanayin daliban da zata koyar.

Daga karshe ta bukaci matsasa da su maida hankali wajen neman ilimi sannan su kauracewa yawan shaye-shayen kwayoyin.

Your browser doesn’t support HTML5

Ta Bukaci Matasa Dasu Maida Hankali Wajen Neman Illimi - Fatima Muhammad 07'22"