Jigo a Jam'iyyar APC, kuma tsohon Shugaban Kasa, Janar Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa mai dauke da sa hannunsa, akan batun Chibok. Ga kadan daga cikin sanarwar.
Daga Janar Muhammadu Buhari
"A makonnin da suka wuce, sace dalibai mata da akayi a Cibok, Jihar Borno ya nuna a fili irin barazanar da muka dade muna fama dashi a kasarnan, daga ayyukan mutanen da basu fahimci Musulunci ba.
Addu’o’in mu suna tare da iyalen wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan tashe-tashen hankula da muke ta gani. Sannan kuma muna mika alhininmu ga iyayen da ‘ya’yansu suke cikin hannun wadannan mugayen mutane.
Wannan mummunan bidiyo da aka saka a yanar gizo, ya nuna a fili cewa shaidanun mutanennan basu da zuciya. Ya nuna ko suwaye su a fili, kuma maza kamar wadanda bai kamata a ce suna keta diyaucin kasa ba. Daga abubuwan da suka nuna, ya fito fili cewa babu Allah a zuciyarsu. Basu da nufin kirki ga kasarmu. Ni Musulmi ne, kuma ina aiki da koyarwar addinin Kirista ma, ta yin amfani da koyarwar addinan guda biyo domin zaman lafiya da kowa da kowa a duniya.
Ina mai sha’awar jaddada matsayi na, na sukar wannan ta’asa wanda bashi da waje duniyar bil-adama. Addinin Musulunci bai amince da shi ba, kuma babu wannan a cikin Bible."