Tukuicin Naira Miliyan 50 Ga Duk Wanda Ya Taimaka Aka Samo Daliban Chibok - 7/5/2014

Takardar fasta ta neman Abubakar Shekau

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce zata bayarda tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka mata wajen samo dalibai mata su 276 wadanda 'yan ta'adda suka sace daga makarantarsu a watan da ya shige.

Rundunar ta ce zata bayar da wannan tukuici ga duk wanda ya ba ta "bayani mai amfani da zai kai ga inda ake tsare da wadannan dalibai da kuma ceto su."

An sanya lambobin wayar da mutane zasu iya kira domin bayarda bayanin wadannan dalibai mata da aka sace daga makarantar sakandare ta Chibok a Jihar Borno ranar 14 ga watan Afrilu.

Rundunar 'yan sandan ta ce za a kare suna da bayanin duk wanda ya tsegunta mata inda wadannan tsagera suke.

Jiya talata, Amurka ta ce zata tura kwararru kan ayyukan leken asiri da na tabbatar da bin doka da oda domin su taimaka wajen samo wadannan dalibai mata.