Mai horar da ‘yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 23, Samson Siasia, ya maye gurbin dan wasan Granada Isaac Success da Victor Osimhen yayin da ake shirin tunkarar gasar ‘yan kasa da shekaru 23 a Senegal.
Siasia ya dauki wannan mataki ne bayan da aka samu tabbacin cewa Isaac din ba zai samu halartar gasar ba.
Osimhen shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zira kwallaye a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 da aka kammala a kasar Chile.
Rahotanni na cewa, wani babban jami’in hukumar NFF ne ya sa a saka sunan Isaac a tawagar ‘yan wasan.
Yanzu haka akwai yuwuwar Najeriya za ta biya kudaden tara ga hukumar kwallon kafa ta CAF, domin wannan canji da za ayi a kurarren lokaci.
A gasar Premier League ta Najeriya kuwa, kungiyar Kano Pillar na shirin sayen karin ‘yan wasa 10 kafin a fara kakar wasa ta shekarun 2015/2016 mai zuwa.
Yanzu haka kungiyar wacce aka fi sani da taken “Sai masu gida”, ta bayyana cewa za ta rike ‘yan wasa 20 daga tsohuwar tawagarta.
Kungiyar ta Kano Pillars dai ta taba lashe kofin gasar sau uku a jere, gabanin su kare a mataki na takwas a kakar wasan da aka kammala.