WASHINGTON, DC —
Kungiyar kwallon kafa ta Voa flamingo dake garin Bauchi ta samu nasaran zuwa wasan kusa da na karshe (Semi final ) a gasar cin kofin matasa na ‘yan kasa da shekaru sha takwas da haihuwa wanda Kungiyar Excellence International Football Academy ta shirya a jihar kano.
Voa flamingo ta samu nasaran zuwa matakin ne sakamakon wasani ukku da suka buga
inda suka sami nasara a wasa daya aka doke su a daya kuma sukayi kunnen doki da kungiyar kwallon kafa ta PPN Academy dake Maiduguri a safiyar alhamis dinnan inda suka tashi 2-2
Gobe idan Allah ya kaimu flamingo zata buga wasan semi final tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Tiki Taka Academy dake Kano a filin wasa na Sani Abacha dake garin Kano, misalin karfe takwas na safe.