Wane Ne Zai Zama Zakaran Gwajin Dafi A Karshen Gasar Russia 2018?

Yayin da ya rage dab da fara fafata wasanninn cin kofin duniya tsakanin kasar Rasha da Saudiyya, jama’a sun dade suna cece-ku-ce akan shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa biyu da suka mamaye duniyar tamaula Ronaldo da Lionel Messi. A ganin ku wane ne zai zama zakaran gwajin dafi a karshen gasar?