Wani Mai Wanke-Wanke Da Ya Mutu, Ya Bar Abun Mamaki

Wata al'umma da ke cikin jihar Vermont a nan Amurka ta yi matukar mamaki, bayan da wani rahoto ya bayyana cewa wani ma'aikacin gidan mai, kuma mai wanke-wanke da shara, bayan barin aikin shi ya mutu.

Sai gashi an samu kudi da ya barwa dakin karatu “Library” da Asibitin garin su, fiye da dalar Amurka miliyan takwas $8M, kwatankwacin sama da naira biliyan biyu.

Ronald Read, ya mutu yana da shekaru 92, yadda ya tara irin wadannan makudan kudaden na da ban mamaki, amma abun da ya fi ban mamaki shine, mutumin da ke da karancin albashi taya zai iya tara irin wannan zunzurutun kudaden.

Amma abun sha’awa da rayuwarsa, bai daukarwa kansa karya ba, ko kuma sayen abubuwa masu tsada ba, ta yadda ya tara kudinsa ke nan, ya kasance mai hakuri, yayi rayuwar mutan Da.

Ga misali mai sauki, yana samun kudin ruwa a shekara-shekara na 10%, lokacin da ya tattara adadin yawan kudin da ya saka sai suka kai $500,000, kashi 10% na wannan zai zama ribar $50,000 a shekara, hakan ya kai shi $550,000.

Lokacin da ya kai dala miliyan 1, koda yake, ribar 10% zai samu $100,000, tare da kai wa ga dala miliyan $1.1. A dala miliyan uku, ribar 10% zata zama dai-dai da kusan $300,000.