Kamar yadda muka tattauna akan dalilan da ke sa wasu iyaye hana 'ya'yan su soyayya ko auren wasu samari a satin da ya gabata, wannan yasa muka nemi jin ra'ayoyin samari da 'yan mata daban daban akan tambaya kamar haka;
Idan ka/ kika sami kan ki/ka a cikin irin wannan hali wato kin amincewar iyaye da soyayya ko aure tsakanin ka da diyar su, wanne mataki zaka dauka?.
Samari da 'yan mata da dama sun bayyana ra'a yoyin su, koda shike yawanci musamman samarin sun nuna cewar tattara ina su ina su, su bar gari tare da amincewar budurwar domin zuwa wani gari a daura masu aure kawai ne mafita. Wasu daga ciki sun nuna neman sa hannun hukuma sa'annan wani daga ciki kuma ya ce shi a nashi ra'ayin zai yi kokrin samun juna biyu da ita.
Da muka waiwaya bangaren 'yan mata kuma, mafi rinjaye sun ce bin nagaba bin Allah, dan haka duk abin da iyaye suka aminta da shi zasu yi amfani duk kuwa da irin zurfin soyayyar da take a zuciyar su.
A garzaya shafin mu na facebook domin bayyana ra'ayi.
Saurari cikakkiyar hirar a nan, Dandalinvoa.com