Wasan Video Game na Kara Hazaka Wajen Karatu

Video Game

Ma’aikatar tarayyar ilimi a kasar Amurika, ta bayyanar da cewar lallai wasan kwamfuta (video game), na taimakawa matuka wajen kara basira da hazakar yara don fahimtar karatu.

Ma’aikatar dai tace wannan wata dama ce, da za’a yima tsarin ilimi gadon bawul, don duba abubuwa da suka kamata a sa, a manhajar karatu, wanda zai sa yara su dinga jin dadin koyon karatu ta hanyar yin amfani da bidiyo game.

A tabakin daya daga cikin jami’in ma’aikatar, Mr. Bryan Crecente, yace idan aka duba rayuwar yara dalibai, za’a ga cewar kamin yaro/ko yarinya su kammala karatun firamari da sakandire, za’a ga cewar sun buga wasan kwamfuta wato bidiyo game, na kimani awowi dubu goma 10,000 wanda yayi dai-dai da yawan awowin da sukeyi a makarantunsu a tsawon shekara.